Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Sa’ad Abubakar na III, ya bukaci ‘yan Najeriya da su amince da wanda ya lashe zaben shugaban kasa a 2023 a matsayin zabin Allah.
Abubakar, wanda ya bayyana hakan a sakonsa na Sallah Eid-el-Fitr ga ‘yan Najeriya a Sokoto, ya bukaci ‘yan siyasa da su rungumi zaman lafiya a kasar nan. a cewar Peoples Gazzete.
“Muna da cikakkiyar masaniyar cewa, babban zabe a Najeriya na gabatowa, Saboda haka, muna kira ga ‘yan Najeriya da su zauna lafiya da juna tare da tabbatar da imanin cewa duk wanda ya fito bayan zabe ba zabinmu kadai ba ne, zabin Allah Madaukakin Sarki.”
Malam Abubakar ya kuma yabawa gwamnatin Sokoto da sauran masu hannu da shuni kan tallafawa mabukata a duk tsawon watan Ramadan.