fidelitybank

Duk wanda ya zama gwamna zamu bi shi – Gawuna

Date:

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce, ko wa Allah ya bai wa mulkin jihar za su bi shi su kuma ba shi shawara, domin ciyar da jihar gaba.

Ɗan takarar ya yi wannan maganar ne a lokacin wata muhawara tsakanin ‘yan takarar gwaman jihar Kano da BBC Hausa ta gabatar ranar Asabar.

Gawuna ya ce ”idan Allah ya so ya ba mu muna addu’ar ya yi riƙo da hannunmu za mu hidimta wa al’umma; idan kuma Allah bai ba mu ba, ko wa Allah ya bai wa za mu bi shi, kuma za mu ba shi shawara ta gaske, domin a samu ci gaban al’ummar jihar Kano”.

Ɗan takarar ya kuma sake nanata kiran al’ummar jihar da cewa a zaɓi cancanta a lokacin zaɓen gwamnan da ke tafe ”a duba mutumin da ya cancanta a zaɓa”.

Ya kuma ce a yi siyasa cikin lumana, domin kuwa ”Mu ‘yan takarar duka da muka zo nan BBC Hausa ta sauke mu a ɗaki ɗaya kuma duka muka gaisa tare da mutunta junanmu”,.

”Dan haka ina kira ga magoya bayanmu da su zauna lafiya” in ji Gawuna.

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp