Dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a zaben gwamnan jihar Kogi na ranar 11 ga watan Nuwamba, Muritala Yakubu Ajaka, a wa ya nisanta kansa daga wata zanga-zangar da magoya bayan jam’iyyarsa suka shirya yi a Lokoja da Abuja a lokaci guda a yau, Asabar.
A wani faifan bidiyo mai tsawon dakika 41 da ya fitar a daren Juma’a, Ajaka, wanda ke neman sakamakon zaben gwamnan jihar Kogi a kotu, ya bayyana cewa wadanda ke shirin gudanar da zanga-zangar a Lokoja da Abuja wakilan jam’iyyar APC mai mulki ne.
Dan takarar Gwamnan na SDP wanda ya fusata ya yi kira ga jami’an tsaro da su kame duk wani mai zanga-zanga da sunan sa ko jam’iyyar sa.
Kalamansa: “Yanzu an sanar da ni wani shirin zanga-zangar da wasu mutane ke da’awar cewa su ‘ya’yan jam’iyyar Social Democratic Party, SDP ne, ko kuma suna aiki da umarnina. Ban ba da izinin wata zanga-zanga a Lokoja ko Abuja gobe, (Asabar).
“Duk wanda ya yi zanga-zanga da sunana a kama shi. Dukkansu wakilan Gwamna Yahaya Bello ne masu kokarin haifar da rudani a jihar da kuma watakila a Abuja.
“Don haka don Allah ya kamata hukumomin tsaro su lura su kama wadannan mutane. Duk wanda aka gani da SDP vest gobe (Asabar) yana zanga-zanga, to a kama su. Wakilan Yahaya Bello ne”.