fidelitybank

Duk wanda ya ke tunzira Isra’ila ya daina – Majalisar Dinkin Duniya

Date:

Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya, Tom Fletcher, ya mayar da martani game da mummunan labarin hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza.

Fletcher, a cikin wani sakon tweet a kan X ranar Talata, ya yi kira ga duk wanda ke da tasiri da ya dakatar da hare-haren.

“Ma’aikatan jin kai sun yi duk mai yiwuwa don ceton rayuka da yawa kamar yadda za mu iya a Gaza kuma yanzu wannan,” in ji Fletcher.

“Duk mai tasiri dole ne ya dage wannan tsayawa.”

Idan dai za a iya tunawa a baya sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun kai hari a yankunan Gaza da sanyin safiyar ranar Talata, lamarin da ya kawo karshen takun sakar da aka shafe makonni ana gwabzawa a tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu a watan Janairu.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza daga baya ta ba da rahoton cewa a kalla mutane 326 ne suka mutu.

Ana sa ran adadin zai karu a cikin sa’o’i masu zuwa yayin da da yawa ke ci gaba da zama a karkashin baraguzan gine-ginen da aka harba.

A cewar ma’aikatar lafiya ta kasar, an sami rahotannin kai hare-hare a wurare da dama, da suka hada da arewacin Gaza, da birnin Gaza, da Deir al-Balah, Khan Younis, da Rafah dake tsakiya da kudancin zirin Gaza.

www.najnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp