Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya yi gargaɗi ga duniya cewa duk ƙasar da ta saka dokar hana shawagin jirage, ya na nufin ta shiga yaƙin Ukraine.
Shugaban na Rasha ya ce, “Za mu ɗauki duk wani mataki da aka ɗauka ta wannan hanyar a matsayin shiga cikin yaƙi a kasar.”
A ɓangaren soji, dokar hana shawagin jirage na nufin babu wani jirgi da zai shiga ko ratsawa ta yankin da ake yaƙi. Duk jirgin da ya ratsa za a iya harbo shi.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya caccaki Nato kan rashin ayyana hana shawagin jirage, ya na mai cewa wannan “rauni ne da rashin haɗin kai.”
Nato a nata ɓangaren ta ce ,wannan zai iya rura wutar yaƙin zuwa wasu ƙasashe.