Gwamnatin Jihar Neja ta ce, za ta bada kudi ga duk wanda ya kawo bayanan sirri dangane da harkoki ‘yan ta’addan da suka addabi jihar.
Sakatariyar yada labaran gwamnan, Mary Noel-Berje, ta tabbatar da hakan cewa, rashin tsaro ya tsananta a jihar, har ta kai ga gwamnatin ta dakatar da wasu ayyukan da take yi.
Mary Neol-Berje, ta ce, rashin tsaro ya zama babban kalubalen da ya addabi jihar hakan ya sanya, Gwamna Sani Bello, ya kawo wannan tsarin a matsayin mafita.
A cewar The Nation, gwamnatin ta bayyana hakan ne domin samar da damar da za ta taimaka wa jami’an tsaro samun bayanan sirri kan masu ta’addanci a jihar