Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce, duk wanda ya ce Najeriya kalau take a halin yanzu yana bukatar a duba lafiyarsa.
Obasanjo ya yi wannan jawabi ne a matsayin babban bako na musamman a wajen taron shekara-shekara na gidauniyar Wilson Badejo karo na 15 mai taken, ‘Kawar da tagwayen kalubale na talauci da rashin tsaro a Najeriya’ da aka gudanar a Legas.
Tsohon shugaban kasar yace, Najeriya bata dauki matakin da ya dace ba saboda talauci da rashin tsaro.
Ya ce, “Najeriya ba inda ya kamata ta kasance a yau. Idan wani ya ce ba daidai ba a inda muke a halin yanzu, to ana bukatar a bincika kan mutumin.


