Gwamnatin jihar Kogi ta bayar da umarnin kamawa tare da gurfanar da wasu mutane da ‘yan kasuwa da suka ki amincewa da tsohuwar takardar naira.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Kingsley Fanwo ya fitar, ta taya ‘yan Najeriya murna kan “hukuncin tarihi na kotun koli”.
A makon da ya gabata ne kotun kolin ta yanke hukuncin cewa duka tsofaffi da kuma sabbin takardun kudi na Naira sun ci gaba da kasancewa a kan doka har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.
Fanwo ya bayyana cewa, gwamnatin Yahaya Bello ta bi sahun sauran jihohi, domin gudanar da shari’ar domin rage wahalhalun da rashin kudi ke fuskanta.
Ya ce ba za a amince da yadda wasu mutane da ‘yan kasuwa ke ci gaba da kin amincewa da karɓar tsofaffin takardun ba, ko da kotu ta tabbatar da amfani da su.
“Kin kin amincewa da tsohon takardun Naira, rashin biyayya ne ga hukuncin Kotun Koli,” Kwamishinan ya jaddada.
“Duk wanda ya ki amincewa da tsohuwar takardar naira a kai rahoto ga hukumomin tsaro da na gwamnati domin daukar mataki cikin gaggawa. Haka kuma, bankunan da suka ki karbar kudaden ajiyar tsohuwar naira, za a rufe su.”
Fanwo ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta karbi cibiyoyin hada-hadar kudi ba “wadanda ke kin bin umarnin kotu da gangan, haka kuma, umarnin kotun koli a Najeriya”.
“Tunda bankunan na fitar da tsoffin takardun kudi na Naira, su ma za su karba. Ba za mu iya ci gaba da kashe tattalin arzikinmu ba bayan Kotun Koli ta ba mu ‘yanci.”
Sanarwar ta sanar da kafa wani kwamiti mai cikakken iko domin tabbatar da cikakken bin doka da kuma aiki da hukuncin.