Gwaman jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya gargaɗi waɗanda gwamnatin jihar ta bai wa aikin raba kayan aikin noman rani da su kauce wa ayyukan rashin gaskiya da “cin amanar da aka ba su”.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ƙaddamar da aikin raba kayan noman rani a garin Wamako na jihar ta Sokoto a ranar Litinin.
Ya ce “Ina gargaɗin ku da kakkausar murya, kada ku ci amanar da aka ba ku kamar yadda ya faru a lokacin damina.
“Mun ɗauki matakan tabbatar da cewa an hukunta duk wanda ya yi yunƙurin karkatar da kayan a wannan karo.
“Ku kasance masu tsoron Alla, ku bari al’umma su amfana da wannan tsari na gwamnati.”
Gwamna Aliyu ya ce gwamnatin Sokoto na ganin cewa babbar hanyar bunƙasa rayuwar al’ummar jihar ita ce ta hanyar bunƙasa ɓangaren noma.
Ya ce gwamnatinsa za ta raba filayen noman rani hekta 450 ga manoma a yankin Kware, sannan an fara aikin noman rani na Wurno yayin da aka bayar da kwangilar farfaɗo da madatsar ruwa ta Lugu Dam.
Noma ne babbar sana’ar al’ummar yankin arewacin Najeriya, sai dai a shekarun baya-bayan nan ɓangaren na noma ya samu koma-baya sanadiyyar matsalar tsaro.