Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ce daurin shekara daya ko tarar Naira 500,000 na jiran duk wanda aka samu da laifin siyan kuri’u a zaben 2023.
Kwamishinan INEC na jihar Jigawa, Farfesa Muhammad Lawal Bashar ya bayyana haka a wata hira da manema labarai.
Kwamishinan ya ce hukumar zabe ta shirya tsaf domin gudanar da dukkan zabukan da na’urar BVAS domin tabbatar da gudanar da sahihin zabe.
” Na’urar za ta tantance masu kada kuri’a da za su kada kuri’a kuma wadanda suka yi rajista fiye da sau daya ba za su iya kada kuri’a ba.
Farfesa Muhammad ya ce Hukumar ta karbi katunan zabe na dindindin sama da dari da hamsin da shida wadanda ake ci gaba da rabawa har zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2023.
Ya shawarci wadanda suka yi rajista amma ba su karbi katin zabe ba da su yi hakan kafin ranar rufewa.
Kwamishinan ya kara da cewa hukumar ta yi kyakkyawan tsari da zai baiwa masu bukata ta musamman da tsofaffi da mata masu juna biyu damar kada kuri’a cikin sauki.