Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari babban ofishin ‘yan sanda dake Okene a jihar Kogi.
A sanarwar da kwamishinan labarai, Kingsley Fanwo, ya fitar ya ce, an kashe mutum ɗaya daga cikin su, sauran sun gudu da raunuka.
Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar su gaggauta kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbin bindiga.
Yan ta’addan sun haura 30, a cewar wata sanarwa da kwamishinan ya ce, ɗaya daga cikin ‘yan bindigan ya gamu da ajalinsa, yayin da sauran suka ranta a na kare ɗauke da raunin alburushi a jikin su.
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin cewa duk yan bindigan da suka shigo jihar ba zasu fita da rayuwarsu ba.