Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta ce, kwastomomin da ba sa samun adadin wutar lantarki na sa’o’i 20 ba za su biya sabon farashin kudin wutar lantarki ba.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin wutar lantarki domin gudanar da bincike na kwana daya kan bukatar dakatar da sabon kudin wutar lantarki.
Ya ce gwamnatin tarayya ta bullo da wata sabuwar manufa ta ceto bangaren wutar lantarki, yana mai jaddada cewa radadin na wucin gadi ne.
Bayanin ya zo ne a daidai lokacin da masu amfani da wutar lantarki ke kokawa kan karin kudin fito da hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya NERC ta yi.
Ministan ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta biya Naira Tiriliyan 2.9 domin tallafa wa wutar lantarki a bana idan ba a sake duba kudin fito ba.
A cewarsa, gwamnati ta bullo da sabuwar manufar ceto bangaren wutar lantarki.