Wata mai mai ƴaƴa tara ta ce, duk runtsi duk wahala ba za ta bar Gaza ba duk kuwa da yunƙurin da Isra’ila ke yi na faɗaɗa yaƙin da take yi a zirin.
Fatma Al-Shinbary mai shekara 41 ta shaida wa Reuters cewa za ta tsaya a zirin domin ta cigaba da rayuwa, sannan ta ƙara da cewa, “mafi yawan mutanen zirin ma ba za su fice ba.”
Mijin Fatima yana kwance ne yana jinya, ita ce take ɗawainiya da gidan ta hanyar saa’anta burodi tana sayarwa a sansanin ƴan gudun hijira da suke zama.
Ta ce ta sha barin inda take zama a shekaru baya da suka gabata, inda ta ce, “na gaji da tsalle-tsalle.”
“Gara mutuwa a gare mu,” in ji ta, sannan ta ƙara da cewa, “a duk inda muka je, idan za mu canja waje, mukan tafi ne mu bar kayayyakinmu, a haka muke ta asarar kayayyakinmu.”