Matan da suka haifi tagwaye a Akwa Ibom za su rika samun tallafin kuɗi naira 50,000, yayin da za a bai wa matan da suka haifi ƴan uku kuma N10,000.
Mai ɗakin gwamnan jihar, Mrs Patience Umo Eno ce ta bayyana haka a lokacin wani taro karkashin shirin karfafawa mata masu haihuwa a jihar.
Da take bayyana batu bayar da tallafin kuɗin a mazaɓar Ikot Ekpene, Mrs Eno ta ce samar da kuɗaɗen alawus-alawus na wata-wata ga waɗanda za su ci gajiyar shirin, an yi shi ne don rage wa iyalai nauyin kula da ƴaƴansu musamman waɗanda ke haihuwa da yawa..
Mrs Eno ta faɗa wa iyaye a mazaɓar Eket da suka haihu da yawa cewa, “Kun ga nagarta da alherin Allah. Yana kyau ku yi murna da abin da Alla ya ba ku kuma shi ya sa muka taru a nan.
“Ina son tagwaye da ‘yan uku shi ya sa na sanya duk abin da zan iya a cikin wannan shiri. Ina so ku ƙara godiya ta hanyar nuna soyayya da kuma kula da yaran nan,” in ji mai ɗakin gwamnan.
Da yake jawabi, shugaban riko na karamar hukumar Ikot Ekpene, John Etim, ya yaba wa uwargidan gwamnan kan yadda ta rika tallafawa al’umma.
Ya ce hakan na taimakawa wajen bunƙasa gwamnatin jihar, inda ya kwatanta Mrs Eno a matsayin uwa mai tasiri a faɗin jihar.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an raba wa matan da suka ci gajiya kayan jarirai da kuma kuɗi.