Kocin Barcelona Xavi ya ce zai ajiye aikinsa a ƙarshen kakar wasanni ta bana.
Tsohon ɗan wasan Barcelona da Spain ya soma aikin koyar da ƙungiyar ne a watan Nuwambar 2021 bayan ya bar Al Sadd ta Qatar.
Ya ci wa Barcelona La Liga a kakarsa ta 2022-23, sai dai dokensun da Villareal ta yi da ci 5-3 a ranar Asabar ya sa yanzu maki 10 ne tsakaninsu da Real Madrid da ke matsayi na ɗaya a gasar.
“Ni ɗan ƙungiyar nan ne. Na fi sonta sama da kai na. Na yi iya iyawata,” in ji Xavi.
“Kuma zan ci gaba da iya ƙoƙarina domin sanyawa magoya baya farin ciki.”
Duk da cewa yana da sauran shekara guda a ƙungiyar, ɗan shekara 44 zai bar aikin a ranar 30 ga watan Yunin wannan shekarar.