Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi ya ce kamata ya yi duk shugabanni da aka samu da cin hanci a Najeriya su riƙa fuskantar tsassaurar hukunci.
Obi ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar yau Talata domin bikin ranar yaƙi da cin hanci ta duniya.
A cewarsa, cin hanci ya dabaibaye dukkan matakan gwamnati a Najeriya a tsawon shekaru.
Ya ce ƙasar na fuskantar tarin bashi da ya yi mata katutu, wanda ya faru sakamakon ciyo bashi da gwamnatoci ke ci gaba da yi.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya shawarci shugabannin Najeriya da su zama masu gaskiya da kuma kauce wa cin hanci da rashawa.
“Ƙasancewar Najeriya a jeri na 145 cikin ƙasashe 180 da aka fi cin hanci, ya nuna yadda rashawa ta yi wa Najeriya katutu. Ya kamata a yaƙi hakan idan ana son ci gaba,” in ji Obi.
Ya ƙara da cewa Najeriya na cikin ƙasashen Afrika 11 da ke fama da rashin kyawun shugabanci a cikin shekara 10 da suka wuce.
Ya ce hakan ya ci gaba da janyo cikas wajen samun cigaba a ƙasar.