fidelitybank

Duk rintsi mu ne za mu samu nasara a jihar mu – Fubara

Date:

Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya bayar da tabbacin cewa bayan duk rikice-rikicen da ake yi na siyasa a jihar, jihar ce za ta ci nasara.

Fubara ya bayyana haka ne a lokacin da ƙungiyoyin addini musulunci, ciki har da ƴan majalisar ƙoli ta addinin musulunci suka kai masa ziyarar gaisuwar sallah a gidansa da ke Fatakwal.

Da yake musu jawabi, Fubara ya ce su yi imani da abin da Allah ya tsara. “Yanzu lokaci ne na nuna ƙauna da sadaukar da kai. Kun zo ne domin nuna mana ƙauna. Na yi imanin cewa duk abin da ya faru Allah ne ya tsara, kuma ina da tabbacin nasara za ta biyo baya,” in ji shi kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

“Duk abin da ke faruwa, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba domin mun yarda da ikon Allah. Na yi imanin cewa mu ne za mu samu nasara. Ko da kuwa akwai zafi da damuwa, ba matsala, abu mafi muhimmanci shi ne tsayawa kan gaskiya.”

A nasa jawabin tun farko, Alhaji Nasir Awhelebe Uhor ya ce sun je ne domin nuna goyon bayansu ga gwamnan, inda ya ce suna tare da shi, kuma suna masa addu’a domin samun nasara.

Ya yi kira ga gwamnan da ya haƙuri, inda ya ce masa Allah yana taimakon masu haƙuri.

nigeria news today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...
X whatsapp