Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa FRSC, Dauda Biu, ya umarci kwamandojin sassan kasa 37 da su kama duk wani babur ba tare da rajistar da ya dace ba.
Biu ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da jami’in kula da ilimin jama’a na Corps Mista Bisi Kazeem ya fitar a Abuja ranar Litinin.
“Dukkan baburan da ba su da rajista za a kama su. Ana bukatar masu baburan su kammala cikakken rajistar baburan kafin a sako su.
“Duk babura da aka kama, dole ne a rubuta cikakkun bayanai,’’ in ji shi.
Shugaban na FRSC ya ce, umarnin ya zama dole ne, biyo bayan karuwar yawan babura da ke bin hanyoyin.
A cewarsa, akwai kuma bukatar a kama duk babura yadda ya kamata a cikin kundin tsarin tantance ababen hawa na kasa.
Ya yi nuni da cewa, umarnin zai taimaka wajen dakile rashin tsaro idan duk baburan da aka kama suna cikin ma’adanar bayanai ta kasa.
Biu ya bukaci kwamandojin sassan da su gaggauta tuntubar hukumomin tattara kudaden shiga na jihohinsu, domin kafa kwamitin da zai magance lamarin.
Ya kuma ba da umarnin cewa, a yi hadin gwiwa da jami’an ‘yan sanda da ofishin binciken ababan hawa da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da aiwatar da aikin.


