Jami’ar yaɗa labarai ta ma’aikatar lafiya ta ƙasar, Ms Patricia Deworitshe ce ta bayar da tabbacin cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Laraba a Abuja, babban birnin Najeriya.
A cewar jami’ar, gwamnati ta sanar da ƙudirinta na ladabtar da duk wanda aka kama da hannu a safarar ƙoda bayan rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa kan yadda ake yin harkar a ɓoye.
Ta ce “ma’aikatar ta yi tir da irin wannan mummunar ɗabi’a ta safarar ƙoda kamar yadda rahoton na Daily Trust ya bayyana.
Ma’aikatar lafiyar ta kuma tunatar da mutane game da sashe na 51 zuwa 56 na dokar lafiya ta ƙasa da ya haramta safarar ƙodar.
“Mutanen da suka ƙi bin dokar sun aikata laifi kuma za su iya fuskantar biyan tarar naira miliyan ɗaya ko zama gidan yari ko ma duka biyun.
Ms Patricia Deworitshe ta ce hukumar kula da aikin likitoci ta Najeriya tana duba zarge-zargen da aka yi kan likitoci da suke wannan ta’adar.
Deworitshe ta ƙara da cewa kamata ya yi bayar da gudummawar ƙoda ya zama bisa masaniyar wanda zai ba da ƙodar tasa, kuma bisa shawarar likita.


