Rasha ta ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a Syria a da safiyar yau Lahadi, yayin da ‘yantawaye suka danna zuwa kudancin ƙasar, kamar yadda ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta ‘Syrian Observatory for Human Rights’ ta bayyana
Hare-haren sun faɗa a yankunan karkara a yankunanIdlib da Hama, inda ‘yantawayen suka zafafa hare-hare a baya-bayan nan.
Gwamnatin Syria ta rasa iko da birnin Aleppo a karon farko tun bayan fara yaƙin basasar ƙasar, kamar yadda masu sanya idanu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.