Joao Santos, wakilin dan wasan tsakiya na Arsenal, Jorginho, ya ce dan wasan yana son ci gaba da zama a tsakiyar kungiyar duk da zuwan Declan Rice daga West Ham.
Jorginho dai ya zo Emirates ne daga Chelsea a cikin watan Janairu.
Sai dai kuma makomarsa ta zama abin hasashe, inda rahotanni suka ce tsohon kociyan kungiyar Maurizio Sarri na neman siyan shi a Lazio.
Sai dai Santos ya shaida wa gidan talabijin na TV Play na Italiya cewa: “Jorginho ya yi matukar farin ciki da Arsenal da ke da muhimmiyar gasar da za ta buga, a farkon watan Agusta akwai Community Shield.”
“Babu wata tattaunawa da Lazio. Ban sani ba ko suna da kudin da za su biya dan wasan, amma wannan ba shine tambayar ba.”