Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya gayyaci dan majalisa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, zuwa wani taron sirri a Abuja.
Ana sa ran Tinubu zai gana da tsohon gwamnan jihar Kano a babban birnin tarayya ranar Laraba.
Wata majiya da ta zanta da DailyNigerian ta bayyana cewa, Tinubu na shirin zawarcin Shekarau cikin jam’iyyar yayin ganawar.
Hakan na zuwa ne bayan rahotanni sun bayyana cewa, Shekarau ya cimma yarjejeniya da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya koma jam’iyyar.
Wata majiya da ta yi magana kan shirin Tinubu na neman Shekarau zuwa APC ta ce, tun da farko dan takarar shugaban kasa ya gana da Shekarau a ranar 8 ga watan Agusta, amma ba a cimma matsaya ba.
Majiyar ta ci gaba da cewa, duk da cewa Shekarau ya amince ya koma PDP, amma tsohon gwamnan ya gayyaci majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, wato Shura Consultative Assembly, don ba shi shawara kan ci gaban.
Ana sa ran majalisar za ta gabatar da rahoto a yau kuma za a sanar da hukuncin a cikin mako guda