Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba ya nadamar goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a kan Jam’iyyar PDP, dan takarar Shugaban kasa, Atiku Abubakar, a zaben 2023.
Wike ya ce wasu daga cikin abokan hamayyar sa sun karbi kudi daga hannun Atiku domin su yi fada amma duk sun kasa.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen liyafar cin abincin sabuwar shekara da ya shirya a gidan sa da ke Obio-Akpor ranar Juma’a.
A cewar Wike: “Bani nadamar goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashe zabe.
“Duk wadannan suna surutu, sun ce wa Atiku, za mu yi fada da shi. Ta yaya mutanen da suka fito suka ce Fubara ba zai iya zama gwamna ba, ba zai iya yin magana a gaban jama’a ba, yau su ne suke cewa muna tare da kai a 2027?
A yayin da ake kara tunkarar zaben shugaban kasa a shekarar 2023, Wike, gwamnan jihar Ribas, ya goyi bayan Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Wike ya ki marawa Atiku baya saboda rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP.
Tsohon gwamnan jihar Ribas ya caccaki matakin da jam’iyyar ta dauka na barin dan takararta na shugaban kasa kuma shugabanta na kasa ya fito daga Arewa.