Yan sanda sun tabbatar da kama wanda ya sace Nabeeha Al-Kadriyah da wasu mutane da ake zargi da hannu cikin satar mutane.
Kakakin ‘yan sandan Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Cikin sanarwar ya ce, a wani samame da suka akai wani otel a yankin Tafa, a ranar 20 ga watan Janairu, sun cafke wani da ake kira Bello Mohammed, ɗan shekara 28, mutumin Zamfara.
“An kama shi da kuɗi da suka kai naira miliyan 2 da dubu dari biyu da hamsin, wanda muke zargin kuɗin fansa ne da wani wanda aka kama ɗan uwansa ya biya a tsukukun yankin.
“Yayin gudanar da tambayoyi, mun gano cewa yana cikin gungun mutane da suka kama iyalan wani lauya da ake kira Ariyo a yankin Bwari da ke Abuja a ranar 2 ga watan Janairu. Wadanda suka kashe wata matashiya da ake kira Nabeeha,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Wanda ake zargin in ji sanarwar ya yi tayin miliyan guda ga shugaban ‘yan sandan yankin, sai dai DPO bai karbi kuɗin ba, ya yi aikinsa yadda ya kamata.