fidelitybank

Duk da na fi kowane dan wasa cin Manchester UTD zan bar Liverpool – Salah

Date:

Mohamed Salah ya ce, wannan ce shekararsa ta ƙarshe a Liverpool kuma babu wanda ya yi masa magana kan sabunta kwantaraginsa a kulob ɗin.

Dan wasan Masar ɗin mai shekara 32 ƙwantaraginsa a Liverpool za ta ƙare ne a ƙarshen kaka mai zuwa.

Ya samu nasarar zira kwallo ɗaya a wasan da suka doke Manchester United da ci 0-3 a ranar Lahadi.

Ana ckin wasan Salah ya rika taka leda tamkar wasan shi ne na ƙarshe da zai buga a Old Trafford.

“Da zan shigo wasan ina jin cewa kamar wannan ne lokaci na na ƙarshe,” ya shaida wa Sky Sports.

“Babu wanda a ƙungiyar ya yi mini magana kan kwantaragina dan haka na ce, to shi kenan, wataƙila a ƙashen kaka na tafi. Za mu ga mai zai faru nan da shekara guda.”

Salah wanda ya ci kwallo a duka wasannin Liverpool uku da suka buga, yana yawan kafa tarihi a Old Trafford:

  • Sala ya ci kwallo 11 ya bayar da shida an ci a gasar Premier a Old Trafford. Ɗan Masar ɗin ya fi kowanne ɗan wasa ci da bayar da kwallaye a ci United a tarihin gasar.
  • Ya ci wa Liverpool kwallo 10 a wasa tara da ya buga a Old Trafford a duka gasa. Shi ne ɗan wasan da ya taɓa cin kwallo 10 zuwa sama a gidan wata ƙungiya a Premier tun bayan tarihin da Alan Shearer ya kafa a 1992-93 a Elland Road.
  • Sala ne ɗan wasa ɗaya tilo da ya ci kwallo a wasanni biyar da ya buga a gasar Premier a gidan United.

today nation

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp