Shugaban Kamfanin sojojin hayar Rasha ‘Wagner’ Yevgeny Prigozhin ya shaida wa gidan talbijin na ‘Afrique Media TV’ cewa sojojinsa za su ci gaba da ayyukansu a inda suke a yanzu a ƙasashen Afirka
“Za mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu a duka ƙasashen da muka fara ayyukanmu” kamar yadda ya bayyana. A cewar BBC.
Ya ƙara da cewa “Duk ƙasar da ta buƙaci taimakon ƙungiyar Wagner a ko’ina domin yaƙar ‘yan tawaye da ‘yan ta’adda, za mu taimaka domin kare ‘yan ƙasar da zarar an amince da sharuɗa da aƙa’idojinmu”.
Mista Prigozhin ya ce ƙungiyar ba ta da niyyar rage ayyukanta a Afirka.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan samun raɗe-raɗin janye dakarun ƙungiyar daga ƙasashen Mali da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, bayan taƙaitaccen boren da ƙungiyar ta yi a Rasha ranar 24 ga watan Yuni.
Kungiyoyin kare hakkin bil-adama na zargin dakarun Wagner da keta hoƙƙokin bil-adama a Mali da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.