Shugabannin mulkin soji a Nijar, sun sanar da naɗa ministoci.
Sojojin sun sanar da haka ne a wata doka da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar a cikin dare.
Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine shi zai jagoranci mambobi 21 na gwamnatin, inda sabbin janar-janar ɗin gwamnatin mulkin sojin za su shugabanci ɓangaren tsaro da kuma harkokin cikin gida. In ji BBC.
Hakan na zuwa ne yayin da ECOWAS ke gudanar da taro yau Alhamis a Abuja domin yiwuwar ɗaukar matakin soja ko bin hanyar diflomasiyya wajen warware rikicin na Nijar.
Tun da farko sojojin na Nijar sun yi watsi da wa’adin da ECOWAS ta ba su na mayar da shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.
Ga cikakken jerin sunayen mambobin majalisar zartarwar gwamnatin mulkin sojin Nijar, kamar yadda Mahamane Roufai Loauali, sakatare-najar na majalisar ya sanar
1. Firaminista kuma ministan kuɗi da tattalin arziki – Lamine Zeine Ali Mahamane
2. Ƙaramin ministan tsaron ƙasa – Laftanar-Janar Salifou Mody
3. Ƙaramin ministan harkokin cikin gida da tsaron al’umma – Birgediya-Janar Mohamed Toumba
4. Ministan matasa da wasanni – Kanar-Manjo Abdourahamane Amadou
5. Ministan harkokin ƙasashen waje da haɗa kan jama’ar Nijar da ke zama a waje – Bakary Yaou Sangare
6. Ministan lafiya da walwalar jama’a – Dr Kanar-Manjo Garba Hakimi
7. Ministan kula da majalisar ƙasa da tabbatar da lafiyar cikin gida – Dr Soumana Boubacar
8. Ministan noma da kiwo – Mahaman Elhadj Ousmane
9. Ministan ilimi mai zurfi da binciken kimiyya da fasaha – Farfesa Mahamadou Saidou
10. Ministar ilimi da koyar da sana’oin hannu da kuma bunƙasa harsunan ƙasa – Elizabeth Cherif
11. Ministan sufuri – Kanar Salissou Mahaman Salissou
12. Ministan muhalli da tsaftace ƙasa – Kanar Maizama Abdoulaye
13. Ministan shari’a da kare yancin dan-adam – Alio Daouda
14. Ministar ƙwadago da samar da ayyukan yi – Aissatou Abdoulaye Tondi
15. Ministan tsare-tsaren ƙasa da samar da gidaje – Salissou Sahirou Adamou
16. Ministan jin ƙai da agajin gaggawa – Aissa Lawan Wandarama.
17. Ministan man fetir da ma’adinai da kuma makamashi – Mahaman Moustapha Barke
18. Ministan yawon buɗe ido da sana’oi – Guichen Agaichata Atta
19. Ministan sadarwa da bunƙasa fasahar zamani – Sidi Mohamed Raliou
20. Ministan kasuwanci da masana’antu – Seydou Asman
21. Ministan harkokin kuɗi a ofishin firaminista – Moumouni Boubacar Saidou