Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ƴan Najeriya cewa, duk da kalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da wasu jam’iyyu ke yi ba zai hana ta miƙa wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu mulki ba.
Da yake magana da manema labarai a ranar Talata, shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, ya ce sun shirya tsaf domin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba.
Mustapha ya ce, ƙarar da wasu jam’iyyu suka shigar kan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da jam’iyyar APC da kuma INEC ba zai dakatar da shirye-shiryen da suke yi ba.
Ya ce tuni shirye-shiryen kwamitin ya yi nisa, inda ya ce an ɗora wa ƙaramin kwamitin tsaro na miƙa mulkin da ya tabbatar da cewa babu wani mahaluki da zai kawo tarnaki ga shirin miƙa mulkin.
A ranar 9 ga watan Febrairun 2023 ne shugaba Muhammadu Buhari ya amince da naɗin kwamitin wanda aka ɗora wa alhakin gudanar da dukkan ayyukan shirin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa.
Mambobin kwamitin sun haɗa da sakataren gwamnatin tarayya wanda shi ne shugaban kwamitin da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Sauran sun haɗa da babban lauyan gwamnatin tarayya da babban sakatare a ma’aikatar shari’a da kuma manyan sakatarori daga waɗannan ma’aikatu na gwamnatin tarayya.