Kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) reshen jihar Kano, Zango Abdu, ya ce hukumar ta shirya gudanar da zaɓen cike gurbi na ƴan majalisa a jihar.
A ranar Asabar ne za a yi zaɓukan cike gurbi na ƴan majalisar jiha a mazaɓar Bagwai da Shanono, da kuma na Ghari (Kunchi) da Tsanyawa a jihar.
Da yake magana da manema labarai ranar Alhamis, Zango ya ce babbar damuwar hukumar bai wuce ƴan siyasar da ke cikin zaɓen, duk da cewa sun sanya hannu kan jarjejeniyar zaman lafiya.
“Babau abin da tashin hankali ke haifar wa a harkar zaɓe, dole ne a bar mutane su zaɓi shugabannin da suke so ba tare da tsangwama ba,” kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ambatoshi yana cewa.
Abdu ya kuma ce an raba muhimman kayayyakin zaɓe da sauran abubuwan da ake ɓukata ga ƙananan hukumomin huɗu gabanin zaɓen.
Kazalika baturen zaɓen ya ce an kammala yi wa mutanen da za su yi aikin zaɓen horo, kuma an samar da cikakken tsaro.