Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya ce tun asali dama yana da ƙwarin gwiwar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar cikin watan Fabrairun da ya gabata, duk kuwa da tsarin sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa a ziyara da ya kai wa sarakunan gargajiya na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Yayin da yake magana kan matsalolin da ya fuskanta a zaɓen shugaban ƙasar da ya kai shi ga nasara, shugaba Tinubu ya bayyana damuwarsa kan matakin taƙaita yawan kuɗi da batun sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi, wanda Tinubu ya ce ”bai yi nasara ba”.
Tinubu ya kuma gode wa sarkin Ijebu bisa shawarar da ya ba shi, game da yadda zai ɓullo wa ƙalubalen a lokacin da ya ziyarci fadarsa a baya.
Ya ce ya yi amfani da ƙwarin gwiwa da sarkin ya nuna masa domin magance ƙalubalen da ya fuskanta a zaɓen.
“An riƙe mana kuɗaɗenmu, batun sauyin kuɗi bai yi nasara ba, abin ya tayar da hankali a lokacin. Ina tuna lokacin da na zo jihar domin samar wa kaina mafita, kamar yadda taken jihar Ogun yake, don haka ko da sauyin kuɗi ko babu za mu yi nasara a zaɓen”, in ji Shugaba Tinubu.
Matakin sauyin kuɗi da CBN ya ɓullo da shi cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata ya haifar matsaloli masu tarin yawa da wahalhalu ga ‘yan ƙasar.
Lamarin da ya sa wasu gwamnonin jihohin ƙasar suka gurfanar da CBN gaban kotun Kolin ƙasar, wadda ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudin har zuwa watan Disamban 2023.
Sai dai tsohuwar gwamnatin ta ce wasu daga cikin dalilan da suka sanya ta ɓullo da tsarin su ne domin rage yawan amfani da tsabar kuɗi tsakanin al’umma da hana amfani da kuɗi wajen sayen ƙuri’a da kuma bunƙasa tsaro.
A farkon watan nan ne dai shugaba Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele daga kan kujerarsa, inda jami’an taron DSS suka kama shi tare da tsare shi a hannunsu.