An fitar da Real Madrid daga gasar Copa del Rey ta bana.
Los Blancos ta sha kashi da ci 4-2 a hannun abokiyar hamayyarta ta birnin Atletico Madrid a daren Alhamis.
Samuel Lino ne ya fara zura kwallo a ragar ‘yan wasan Diego Simeone, kafin Jan Oblak da kansa ya zura kwallo 1-1.
Alvaro Morata daga nan ne ya farke masu masaukin baki da dama, amma Madrid ta sake farkewa da kai ta hannun Joselu.
An tashi wasan ne a karin lokaci, inda Antoine Griezmann da Rodrigo Riquelme suka zura kwallo a ragar ta.
Da yake magana bayan wasansu na 21 ba tare da an doke su ba, kocin Madrid Carlo Ancelotti ya ce, “Babu wanda ya cancanci rashin nasara.
“Mun ba da komai. Ina tsammanin a ƙarshe babu wani abin zargi. Dole ne mu duba gaba.
“Mun bar wannan wasan da kyakkyawar fahimta.”


