Jam’iyyar shugaban ƙasar Laberiya George Weah, Coalition for Democratic Change (CDC), ta yi zargin cewa jam’iyyar adawa ta tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu da aka gudanar a makon da ya gabata.
Sai dai, jam’iyyar ta ce duk da cewa ta fito da batun, amma ba za ta kai batun gaba ba saboda tana son ganin haɗin-kai ya ci gaba da wanzuwa a Laberiya.
Shugaba Weah ya amsa shan kaye a ranar Juma’a da ta gabata lokacin da sakamako ya nuna cewa abokin takararsa, Joseph Boakai, yana kan gaba da karamar tazara.
Sakamakon karshe na zaɓen da aka fitar a ranar Litinin, ya nuna cewa Boakai ya samu nasara da kuri’u sama da 20,000.
Ƙungiyoyin sa ido kan zaɓe a ciki da wajen ƙasar, ciki har da ƙungiyar Ecowas da Tarayyar Turai, dukkansu sun ce zaɓukan sun gudana lami lafiya kuma cikin gaskiya.
Sai dai wani taron manema labarai da babban-sakataren jam’iyyar CDC Jefferson Koijee ya kira a ranar Laraba, ya ce jam’iyyarsa tana da hujjoji da ke nuna cewa ɓangaren adawa ya tafka maguɗi.
“Muna da kwararan hujjojin cewa an tafka maguɗi a zaɓen,” in ji shi.
Jam’iyyar Unity ta mista Boakai ba ta mayar da martani kan zarge-zargen ba.
A wani jawabinsa da ya watsu ko’ina a makon da ya gabata, mista Weah ya ce “Al’ummar Laberiya sun yi kira kuma mun amsa kiransu” kuma lokaci ne na amsa shan kaye, lokaci kuma na sanya buƙatar ƙasarmu a farko.
Sai dai ya ƙara da cewa CDC za ta ci gaba da zama babbar jam’iyyar adawa. Zai sauka daga kan mulki ne a watan Janairu.