Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Australia, inda suka rufe babbar gadar Sydney Harbour ta ƙasar.
Sun gudanar da zanga-zangar ce kwana ɗaya bayan kotun ƙolin ƙasar ta amince a gudanar da gangamin a ranar Lahadi, duk da mamakon ruwan sama da aka tashi da shi.
Sun ɗaga kwalaye da ke ɗauke da rubuce-rubuce, suna kira ga ƴansiyasa da su sa baki domin kawo ƙarshen yaƙin a Gaza.
Shugaban WikiLeaks, Julian Assange na cikin waɗanda suka shiga zanga-zangar, tare da ɗanmajalisar ƙasar, Ed Husic.
A shekarar 2023 ne aka taɓa rufe gadar Sydney Harbour na ƙarshe, lokacin da kusan mutum 5,000 suka gudanar da zanga-zanga.
“Mutanen sun riƙa cewa “Isra’ila kin ji kunya, Amurka kin ji kunya. Muna so a kawo ƙarshen yaƙin.”
“An kasa ƙaƙaba wa Isra’ila takunkumi duk da abin da take yi,” in ji wata mai suna Zara Williams da ta halarci zanga-zangar ɗauke da yarinyarta.