Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE ta sake sanya wasu dokoki masu tsauri ga ‘yan Najeriya da ke neman bizar shiga ƙasarta domin yawon buɗe ido ko ziyarar wucin-gadi.
Sanarwar da ƙasar ta fitar ta haramta bai wa ‘yan Najeriya bizar wucin-gadi.
Sannan ɗuk wani ɗan Najeriya mai shekaru 18 zuwa 45 ba za a ba shi bizar shiga ƙasar ba, sai tafiyar ta kasance da iyali.
Wannan na zuwa ne kusan shekara ɗaya da UAE da Najeriya suka shawo kan matsalar haramcin bizar na shekara biyu da aka kakabawa ‘yan Najeriyar.
Amma dage haramcin ya zo da dokoki masu tsauri yanayin da ala tilas ya takaita wa ‘yan Najeriya shiga ƙasar.
Rahotanni na cewa a kullum batun samawa ‘yan Najeriyar bizar UAE na kara zama matsala cike da kalubale.
A yanzu dai wannan sabon doka na nufin an soke ba wa ‘yan Najeriya bizar wucin-gadi baki ɗaya
Sannan ga wanda ya haura shekara 45 idan yana neman biza sai ya gabatar da takardar bayanan asusun ajiyarsa na banki na tsawon wata shida, wanda zai nuna yana da kuɗaɗen da suka kai dala dubu 10 a lokacin neman bizar.
Sai kuma bukatar gabatar da Otel din da mutum zai yi masauki da kuma wasu bayanai na fasfo.