Lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya yi zargin cewa, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi shiru a kan gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Falana wanda ya kasance bako a Siyasa A Yau, wani shirin gidan Talabijin na Channels TV ya yi ikirarin cewa an zarge Emefiele shiru ne bisa zargin bada kudin ta’addanci.
Ya koka da cewa irin wannan mataki na iya faruwa ne kawai a jamhuriyar ‘banana’.
Falana yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa ya ce, “Ba zan iya cewa ba tare da fargabar cewa Mista Godwin Emefiele ba ya nan Nijeriya amma a shiru-shiru jami’an tsaro na jihar suka ce suna neman sa.
“Hakan na iya faruwa ne kawai a jamhuriyar Ayaba inda za a tuhumi Gwamnan CBN da wani babban laifi, wanda shine tallafin ta’addanci,” inji shi.
Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) na fuskantar zarge-zargen kudaden ayyukan ta’addanci, karkatar da kudaden shiga, rancen noma da kuma ayyukan zamba a hada-hadar kasuwanci ta Forex kuma ya kasa zuwa majalisar dokokin kasar domin bayyana dalilin da ya sa aka yi wa naira kwaskwarima da kuma takaita fitar da kudade.