Hukumar tsaro ta DSS ta saki tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC bayan shafe sama da kwana ɗari a hannun hukumar.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a daren ranar Alhamis, DSS ta tabbatar da sakin tsohon jami’in na EFCC.
DSS dai ta kama Abdulrasheed Bawa ne a ranar 14 ga watan Yunin bana, kuma tun daga lokacin take tsare da shi a hedikwatarta da ke birnin Abuja.
A jiya Laraba da dare ne hukumar ta saki Bawa, wanda rahotanni ke cewa ana binciken shi da aikata ba daidai ba a aikin sa.
An dai riƙa yaɗa wani bidiyo da ke nuna shigar Abdulrasheed Bawa gida, inda iyalai da ƴan uwa ke taya shi murna da farin ciki.


