Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya, Aisha Ahmad, bisa zarge-zargen damfarar hannun jari a bankin Polaris da bankin Titan (Union Bank).
Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya shaidawa gidan talabijin na Channels a ranar Lahadin da ta gabata cewa ba zai iya tabbatarwa ko musanta cewa Ahmad na hannunsu ba ko kuma an gayyace shi domin amsa tambayoyi.
A halin da ake ciki kuma, a cewar rahotannin da ke zagaye, ana kuma yiwa Aisha tambayoyi kan yadda bankin Titan ya tara dala miliyan 300 domin kammala sayan bankin Union a shekarar 2022.
A yayin da yake magana kan lamarin, Afunaya ya bayyana cewa, a duk wani bincike da ake yi, ana iya gayyato mutane domin yi musu tambayoyi, kuma ana gudanar da wannan gayyata ne bisa tsarin doka.
Wannan na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan da hukumar sirri ta kama tsohon shugaban Ahmad a babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele. Tun a lokacin yana hannun DSS.
Platinum Post Hausa ta tuna cewa, an dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN a ranar 9 ga watan Yuni.


