fidelitybank

DSS ta bankaɗo wani shirin haddasa rikici da ake kokarin yi a yankin Arewa ta tsakiya

Date:

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bankado wani shiri na haddasa rikici a sassan kasar nan, musamman a yankin Arewa ta tsakiya.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar DSS, Peter Afunanya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Sai dai ya ce an dauki matakan dakile wannan shiri na wasu marasa kishin al’umma.

“Yayin da ke kallon makircin a matsayin rashin kishin kasa, tana kan hanyar jami’an tada zaune tsaye wadanda ke da sha’awar yin amfani da tashin hankali don cimma munanan manufofin.

“Duk da cewa ta sanya matakan kawo cikas ga wadannan dabi’un, ta na gargadin shugabannin da ‘yan kungiyarsu da su kaurace wa ayyukan da za su iya haifar da karya doka da oda,” in ji shi.

Afunanya ya ce an shirya shirin ne domin haifar da rikicin kabilanci da addini, da tayar da kayar baya da kuma zafafa harkokin siyasa.

A cewarsa, a kokarin ganin an cimma hakan, wadanda suka dauki nauyin haka, sun tara mutanen su tare da gudanar da tarurruka da dama a ciki da wajen wuraren da za a kai harin.

Ya ce hukumar ta na sane da wani shiri na yin amfani da dalibai, malaman jami’o’i da ke yajin aiki, kungiyoyin kwadago, marasa galihu da kuma wasu kungiyoyi domin haddasa rikicin.

A cewar Afunanya, manufar kuma ita ce a yi amfani don gudanar da zanga-zangar gama gari kamar # ENDSARS, duk da kokarin da gwamnati ke yi na magance matsalolin.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp