fidelitybank

DSS sun rufe ofishin EFCC na Legas

Date:

Jami’an hukumar ƴan sandan ciki ta Najeriya DSS, sun yi wa ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a Lagos dirar-mikiya inda suka hana jami’an na EFCC shiga ofishin a Ikoyi.

Kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito cewa daman akwai sabani a tsakanin hukumomin biyu a kan wadda a tsakaninsu ta mallaki ginin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wani jami’in DSS ya fada mata bisa sharadin boye sunansa cewa daman sun dade suna takaddama da EFCC a kan wadda ta mallaki ginin, wanda su DSS ne suke amfani da shi tun ma kafin a kirkiri EFCC kuma ya ce an mallaka wa DSS din.

Jami’in ya kara da cewa batu ne da yake a tsakanin hukumomin biyu, kuma bai je gaban shari’a ba sannan ba su taba rikici a kai ba kafin yanzu.

”To amma yanzu ba mu san dalilin da suka zo suka hana jami’anmu shiga ofishin ba, duk da cewa ga sabuwar gwamnati ta zo,” in ji shi.

Jaridar ta ce duk kokarin ji daga bakin masu magana da yawun hukumomin biyu Wilson Uwujaren na EFCC, da kuma Dr Peter Afunaya na DSS a kan batun bai yi nasara ba

guardian newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp