Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama wani dan jarida mai bincike, Adejuwon Soyinka.
Soyinka shine Editan Yanki na The Conversation Africa.
An bayyana cewa an kama shi ne a lokacin da ya isa filin jirgin sama na Muritala Muhammed da ke Legas a ranar Lahadin da ta gabata, ta hanyar jirgin Virgin Atlantic daga kasar Ingila.
Kawo yanzu dai babu wani dalili da hukumar tsaro ta bayar na tsare shi.
Shi ma Soyinka ba a samu ba, saboda an kasa amsa sakonni da kiran wayarsa