Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS, sun cafke Sarkin masarautar Akoh na jihar Ribas, mai martaba Eze Ikegbidi.
Kamen wanda aka gudanar a ranar Litinin din da ta gabata ya biyo bayan wani mummunan kisan gilla da wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar ne suka yi wa jami’in ‘yan sanda reshen Ahoada, Bako Angbashim.
A daren Juma’a ne maharan suka kashe DPO tare da fille masa kai a wani samame tare da mutanensa a yankin.
Kame Ikegbidi da jami’an DSS suka yi ya biyo bayan dakatarwar da gwamnan jihar, Siminilayi Fubara ya yi masa na tsawon lokaci.
Gwamna Fubara a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya zargi sarkin da “bawa shahararren David Gift wanda aka fi sani da 2-Baba da ‘yan kungiyarsa su gudanar da ayyukansu cikin walwala.
Gwamnan ya kuma bayar da ladar Naira miliyan 100,000,000 ga babban wanda ake tuhuma, inda ya ce duk wanda ke da bayanai masu amfani da za su kai ga kama shi da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya to ya kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa.
An tattaro cewa daga baya an mika sarkin ga hukumar leken asiri da binciken manyan laifuka ta jihar dake Fatakwal, babban birnin jihar domin yi masa tambayoyi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, DSP Grace Iringe-Koko, ta ce ba ta da cikakken bayani kan kamun.


