An kama Aisha Galadima, babbar aminiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a siyasance a Kaduna.
Kamen, kamar yadda wata majiya ta shaidawa DAILY POST, yana da alaka da wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda take sukar gwamna Uba Sani.
Jamiāan hukumar tsaro na farin kaya ta DSS ne suka dauke āyar siyasar daga gidanta da yammacin ranar Lahadi.
Daya daga cikin āyan uwanta ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, āYanzu haka DSS ta kama Aisha a gidanta na Tudun Wada da ke Kaduna.ā