Lauyoyin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele, sun koka kan yadda ma’aikatan gwamnatin tarayya ke shirin sake kama wanda suke karewa duk da belin da wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta ba shi.
A cewar gidan talabijin na Channels, babban lauyan Najeriya (SAN), Joseph Daudu, ya bayyana hakan jim kadan bayan zaman kotun a Legas.
Kotu ce ta bayar da belin Emefiele kan kudi Naira miliyan 20 bayan gurfanar da shi gaban kuliya bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Daudu ya yi zargin cewa a halin yanzu hukumar ta DSS ta daura damarar sake kama Emefiele duk da hukuncin.
Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, har yanzu gwamnan CBN da aka dakatar yana can a cikin dakin shari’a tare da lauyoyinsa.


