fidelitybank

DSS ku yi a hankali za a iya kai hari Abuja – Amurka

Date:

Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta mayar da martani kan sanarwar tsaro da ofishin jakadancin Amurka ya fitar na cewa za a iya kai harin ta’addanci a Abuja cikin makon nan.

Ofishin Jakadancin Amurka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya lissafa wuraren da ka iya kai hari kamar gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni, kantuna, otal-otal, da mashaya.

Da take mayar da martani, Hukumar ta yi kira da a kwantar da hankula tare da yin kira ga ‘yan Najeriya da su yi taka tsantsan bayan gargadin.

Ta kuma ba da tabbacin cewa za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin wanzar da zaman lafiya sannan kuma ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanai masu amfani dangane da barazana da kuma ayyukan muggan laifuka a kusa da su.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta samu tambayoyi da dama dangane da shawarwarin tsaro da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya bayar, a yau 23/10/22. Jama’a na iya tunawa cewa Sabis ɗin ya ba da irin wannan gargaɗi daban-daban a baya.

“Hukumar ta yi kira da a kwantar da hankula yayin da take aiki da sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ciki da wajen Abuja.”

daily post newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp