Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Didier Drogba, ya ce masu sha’awar kwallon kafa sun yi tsammanin dan wasan gaba na Paris Saint-Germain Kylian Mbappe zai bar gasar Ligue 1 nan gaba zuwa wata kungiya a gasar Premier.
Kwanan nan Mbappe ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da PSG a bazara yayin da ya ki komawa Real Madrid.
An kuma alakanta dan wasan na Faransa da komawa gasar Premier lokacin da kwantiraginsa da PSG ta kare.
Da aka tambaye shi ko Mbappe na bukatar barin PSG zuwa babbar kungiya a gasar firimiya a kokarinsa na cika burinsa, Drogba, wanda ke aikin kula da harkokin wasanni na BBC ya ce, “Ina ganin abin da dukkan mu muke sa ran zai yi ke nan, amma. Na san shi kadan kadan kuma yana son yin bayani ta hanyar lashe gasar zakarun Turai tare da PSG.”