Mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APCr.
Gawuna ya doke abokin hamayyarsa, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ne ya lashe zaben fidda gwanin da aka yi a daren ranar Alhamis, a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata, Kano.
Da yake bayyana sakamakon zaben shugaban kwamitin zaben fidda gwani na gwamnan jihar, Sanata Tijjani Yahaya Kaura ya ce Gawuna ya samu kuri’u 2,289, yayin da dan takarar Sha’aban ya samu kuri’u 30.