Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da mutuwar wani jami’in ‘yan sanda mai suna DPO mai kula da ofishin ‘yan sanda na Ijanikin, CSP Bolaji Olugbenga.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da hakan a daren Juma’a.
Sai dai Hundeyin bai bayar da cikakken bayani kan jami’in da abin da ya kai ga mutuwarsa ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, ya tattaro a baya cewa DPO din ya ruguje ne a ofishin kuma ya mutu kafin a garzaya da shi asibiti.
An ci gaba da cewa labarin rasuwarsa ya jefa jami’an da ke ofishin cikin jimami.
Wata majiya daga sashen ta ce an kai gawar jami’in zuwa dakin ajiyar gawa.