Borussia Dortmund na iya asarar kudi idan ta doke Real Madrid a wasan karshe na gasar zakarun Turai na bana.
Hakan ya faru ne saboda yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu na cinikin Jude Bellingham a bazarar da ta gabata.
Yarjejeniyar Bellingham da Real ta kunshi wasu sharuddan da suka shafi gasar zakarun Turai, kamar yadda Rhur Nachrichten ya ruwaito.
Idan dan wasan tsakiya na Ingila ya dauki kofin Turai tare da Madrid, to Los Blancos za ta kara biyan fam miliyan 4.3 ga Dortmund.
Dole ne a sake biyan fam miliyan 1.7 idan Bellingham ya shiga cikin kungiyar da ta fi fice a gasar zakarun Turai.
Wanda ya yi rashin nasara ya samu fam miliyan 12.9 a cikin kudin kyauta, wanda zai kai fam miliyan 19.3 ga Dortmund idan aka kara da kari ga Bellingham.
Idan Dortmund ta yi nasara a Landan wata mai zuwa za ta samu kasa da wannan kudin, inda za a ba da kyautar £17.2m ga wanda ya yi nasara.