Kungiyar Doma United, ta sanar da bacewar mai tsaron ragarta Abdullahi Zalli.
A wata sanarwa da kungiyar da ke Gombe ta fitar a ranar Juma’a, Zalli ya tafi ne tun ranar Litinin 13 ga watan Maris.
Dan wasan, a cewar kulob din, ya bar sansanin kungiyar ba tare da izini ba.
Zalli kuma ya kasa kulla alaka da kulob din, tun bayan bacewarsa kwatsam.
Kungiyar ta Doma United ta yi gargadin cewa duk wani kulob ko wakili da zai tuntubi Zalli domin yin cinikinsa ba tare da amincewar su ba na fuskantar hadarin kara a gaban kuliya, domin kuwa dan wasan ya kulla yarjejeniya da su.
Kungiyar kwallon kafa ta Savannah Tigers ta fara haskawa a gasar firimiya ta Najeriya a bana.