fidelitybank

Dole sai Emefiele ya sauka daga mukaminsa kafin tsayawa takarfa – Kotu

Date:

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ki yarda da bukatar Gwamnan Babban Bankin kasa na (CBN), Godwin Emiefele ta ba shi kariyar neman takarar shugaban kasa ba tare da ya sauka daga kujerarsa ba.

Mista Emiefele dai ya gabatar da bukatar kotun ta ayyana cewa, yana da damar neman takarar shugabancin a karkashin duk jam’iyyar da yake so, yayin da yake rike da mukamin gwamnan bankin.

Tun da farko a yau Litinin lauyan Emiefele, Mike Ozekhome, ya bukaci kotun da ta amsa bukatarsu ta bayar da umarni na wucin-gadi na hana Hukumar Zabe ta Najeriya (INEC) da Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a na Tarayya daga hana shi shiga zaben fitar da gwani na duk jam’iyyar da yake so.

Da yake zartar da hukunci, alkalin kotun Ahmed Mohammed, ya ayyana cewa, maimakon haka sai dai ya umarci hukumar zaben da Babban Lauyan su bayyana a gabanta ranar 12 ga watan Mayu domin su bayar da bahasinsu kan dalilin da suke ganin kotun bai kamata ta amsa bukatar Mista Emiefele ba.

A zaman na yau Litinin, lauyan gwamnan ya ce zuwa ranar Laraba 11 ga watan Mayu, wa’adin karbar takardar bayyana sha’awar yin takarar shugaban kasar zai kare

A ainahin karar da lauyan Gwamnan Babban Bankin ya gabatar ranar biyar ga watan Mayu, 2022, lauyan ya ce babu wata dokar kasar da ta hana Mista Emiefele takara yana rike da kujerar shugabancin bankin.

Ana matsa wa Mista Emefiele lamba ne da ya sauka daga mukami tun bayan da bayanai suka bayyana na aniyarsa ta neman takarar shugabancin kasar a jam’iyya mai mulkin kasar, APC, a farkon shekarar nan.

A watan Fabrairu na shekara mai zuwa ne 2023, za a yi babban zaben kasa a Najeriya, inda za a zabi wanda zai gaji Shugaba Muhammdu Buhari wanda zai kammala wa’adinsa na biyu na shekara hudu-hudu.

opra news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp